Babu kima da darajar Shugaba Buhari da ta rage a idon ‘Yan Najeriya – PDP

Babu kima da darajar Shugaba Buhari da ta rage a idon ‘Yan Najeriya – PDP

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta dawo da Shugaban NHIS aiki

- Jam’iyyar adawa tace Yusuf Usman ya zari Biliyan 10 a boye

- PDP tace yanzu kowa ya gana irin barnar da Buhari ya tafka

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari gamu da suka daga Jam’iyyar adawa na PDP inda tayi kaca-kaca da kokarin Shugaban kasar na hana binciken da ake yi a Ma’aikatar NHIS.

Babu kima da darajar Shugaba Buhari da ta rage a idon ‘Yan Najeriya – PDP

Jam'iyyar adawa PDP tayi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Jam’iyyar adawar kasar ta soki Shugaba Buhari na dawo da Shugaban NHIS Farfesa Yusuf Usman bakin aiki duk da zargin da ke kan sa. PDP tace babban Sakataren Ma’aikatar NHIS ya zari Biliyan 10 daga asusun Gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Duk wata Gwamnatin Buhari na adana kusan Biliyan 25

PDP ta bakin Mai magana da bakin ta Kola Ologbondiyan ta daura hujjan ne kan zargin da ke kan Farfesa Yusuf Usman na zarar Naira Biliyan 5 har sau biyu daga babban bankin kasar na CBN wanda ke karkashin Shugaban kasa.

Oologbondiyan yace Gwamnatin Buhari na yaudarar Jama’a ne kurum da sunan yaki da sata yayin da ta ke sace kudin al’umma ba tare da an ankara ba. PDP tace yanzu babu wani kwayan martaba da ta ragewa Shugaban Kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel