Amurka da wasu kasashen za su rage sayan man fetur na Najeriya daga shekarar 2022

Amurka da wasu kasashen za su rage sayan man fetur na Najeriya daga shekarar 2022

- Kasar Amurka da wadansu Kasashen za su yi watsi da sayen man fetur daga Najeriya

- Hakan zai faru ne bisa hasashe na cewar Amurka za ta zama fitacciyar mai fitar da mai nan da shekaru 4

- Tabbatuwan hasashen ya danganta ne daga farashin danyen man fetur

Da yuwuwan Amurka da wadansu kasashen sun kusa yin watsi da man fetur na Najeriya, wanda hakan zai kawo cikas ga tattalin arzikin ta. Labari ya zo ma jaridar Vanguard daga EIA (Energy Information Administration), cewar Amurka za ta matukar rage sayen man fetur din Najeriya ya zuwa shekarar 2022.

Amurka da wasu kasashen za su rage sayan man fetur na Najeriya daga shekarar 2022

Amurka da wasu kasashen za su rage sayan man fetur na Najeriya daga shekarar 2022

Za ta yi hakan ne bisa hasashen ta na zama babbar mai fitar da kuma sayarwa kasashe man fetur nan da shekaru hudu. Legit.ng ta lura da cewar a bayanai da EIA ta fitar na wannan shekara, hasahen na Amurka zai tabbata a 2020 ne ma idan farashin danyen mai ya hauhawa.

KU KARANTA: Za mu amshe ragamar mulkin Najeriya a shekarar 2019 - Shugabanin yankin kudu

Idan kuwa farashin danyen mai ya yi arha, to hasashen ba zai tabbata ba har ya zuwa shekarar 2050. Don kuwa farashin sa shi ne ma'aunin shige da ficen sa. Tun a 2017 ne dai Kasar Indiya wacce ita ce ta fi ko wace Kasa sayan mai na Najeriya, ta koma sayen na Amurka.

Game da hakan ne Ciyaman din Kungiyar Albarkatun Man Fetur na Najeriya, Bank Anthony Okoroafor, ya ce mafita ita ce a nemo wasu ma su sayen kuma a inganta harkar man fetur din. Ya ce idan a ka gina matatu a ka kuma habaka lamarin, tattalin arziki zai bunkasa, ayyukan yi za kuma su samu.

A wani zancen na daban, Legit.ng ta kawo ma ku rahoton cewa Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya ce Sakatare Janar na Kungiyar Kasashe ma su Fitar da Man Fetur (OPEC), mai suna Muhammad Barkindo, zai ziyarci Najeriya kwanan nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel