Bamu yarda da samar da yan sandan jiha ba - Kungiyar Arewa Consultative Forum

Bamu yarda da samar da yan sandan jiha ba - Kungiyar Arewa Consultative Forum

Kungiyar mashawaratan Arewa a yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu ta bayyana rashin yardanta da samar da hukumar yan sandan jiha a Najeriya.

Zaku tuna cewa gwamnonin jihohi 36 sun goyi bayan samar da hukumar yan sandan jiha domin dakile rashin zaman lafiyan da ke faruwa a fadin kasa.

Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ne bayan goyon bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Amma kungiyar mashawartan Arewa, ACF ta bayyana cewa mara goyon bayan yan sandan jiha dda gwamnoni suka yi, wani sinadarin haifar da sabbin rikici ne.

Sakataren kungiyar, Anthony Sani, a wani hira da manema labarai a Kaduna ya bayyana cewa idan har aka kuskura aka kafa, gwamnoni zasuyi amfani da wannan damar domin zalunci kamar yadda sukeyi da zaben jiha.

Bamu yarda da samar da yan sandan jiha ba - Kungiyar Arewa Consultative Forum
Bamu yarda da samar da yan sandan jiha ba - Kungiyar Arewa Consultative Forum

Game da cewar ACF, gwamnoni da ke kan karagar mulki zasu yi amfani da yan sandan wajen zaluntan yan adawansu.

KU KARANTA: Makiyaya suna ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

“Bisa ga kwarewa sa ilimin yadda gwamnatocin jiha suke amfani da hukumomin zaben jiha wajen kashe demokradiyya inda jam’iyyar adawa basu iya cin zabe a kananan hukumomi, akwai yiwuwan haka ya faru idan aka samar da yan sandan jiha."

Kungiyar ACF tace matsalan hukumar yan sanda rashin kayan aiki ne da kuma rashin isasshen jami’an yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: