2019: Gwamna El-Rufai zai ga karshen siyasar Sanata Hunkuyi
- Gwamnan Kaduna ya shiga takun-saka da wani Sanatan Jihar
- El-Rufai ya maidawa bangaren Jam’iyyar APC a Kaduna raddi
- Nasir El-Rufai yace za su ga karshen ‘yan siyasa irin su Hunkuyi
Nasir El-Rufai zai yi ta ta kare da Sanatan Arewacin Jihar Suleiman Othman Hunkuyi. Gwamna yace Sanatan na neman suna ne kurum yake burga cewa su ne su ka daura shi a kan kujerar sa a 2015 bayan shi Sanatan ya nemi Gwamnan tun 2003 bai samu ba.
Gwamna El-Rufai ya lissafo irin nasarorin da ya samu a hawan sa mulki. Gwamnan yayi haka ne domin maida martani ga sukar sa da wani bangare na APC tayi. Gwamnan yace ya gyara ilmi ya kuma fadada hanyoyin samun kudin shiga sannan ya ba Matasa aiki.
KU KARANTA: Sanata Shehu Sani sun kai wa Buratai ta'aziyya
Mai magana da yawun Gwamnan watau Samuel Aruwan yayi raddi ga kalaman Sanata Hunkuyi wanda ya sha alwashin ba Gwamnan kashi a 2019. Mai Girma El-Rufai yace su za su karshen duk wani karuwan ‘Dan siyasa a Kaduna irin su Sulaiman Hunkuyi.
A cewar Gwamnan, babu dalilin biyewa Sanatan don kuwa yanzu ba a ma a ta ta su don an ga aiki a Gwamnatin sa. Yanzu haka dai Jam’iyyar APC ta samu kan ta cikin rabuwa a Jihar ta Kaduna wanda Gwamnan yace bai dace wasu kurum su bangare daga Jam’iyya ba.
malu
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng