2019: Wata Kungiya ta gano makircin da ‘Yan Majalisa ke shiryawa Shugaban kasa
- ‘Yan Majalisa na nema su canza yadda za a gudanar da zabe na 2019
- Wata Kungiya tace Shugaban Kasa Buhari ake neman ayi wa makarci
- An yi kira ga Shugaba Buhari ya guji sa hannun sa kan wannan kudiri
‘Yan wata Kungiya ta Masoyan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Inyamurai tayi tir da yunkurin Majalisa na canza tsarin yadda za a gudanar da zaben 2019 inda su kace akwai wata kullalliya ne a kasa da ake shiryawa Shugaban kasar.
Labari ya zo mana daga Jaridar Vanguard inda Magoya bayan Shugaban kasar su kace Majalisa na shiryawa Shugaba Buhari wata kulalliya ne game da zabe mai zuwa don haka su kace Shugaban kasar ya guji sa hannu a kudirin da zai sauya tsarin zabe.
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin ganin an daina zubar da jini inji Malamai
Kungiyar da ke tare da Shugaban kasar tace yunkurin da Majalisa ke yi ya nuna cewa tana da wata manufa a boye kuma Majalisa ma ba ta bata damar fitar da lokacin da za a gudanar da zabe. Wannan Kungiya tace INEC kadai ke da wannan hurumi.
Dokar kasa dai ta ba Hukumar zabe mai zaman kan ta watau INEC kadai ne damar sa ranar zabe da gudunar da zaben. Sai dai Majalisa na kokarin juyo da zaben domin a fara yin na ‘ya ‘yan ta sannan ayi zaben Shugaban kasa bayan na Gwamnonin Jihohi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng