Kotu ta dage shari’an da akeyi da mai kwaikwayon Buhari

Kotu ta dage shari’an da akeyi da mai kwaikwayon Buhari

Wata kotun majistare dake Kano tace zata saurari shari’an wannan mutumin da ya dade yana ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen, wato , Abdulmajid Danbilki-Commander a ranar 30 ga watan Mayu.

Mai shari’a, Kabiru Abubakar, ya dage sauraron shari’an a lokacin da aka zo zama a ranar Alhamis.

Danbilki-Commander, mai shekaru 58, wanda ke zaune a unguwar Koki Quarters, bai amsa tuhuma uku da ake masa ba na tozarci da gangan, bata suna da kuma tsokana.

Wanda ya shigar da karan, Mista Sunday Ekwe, ya fada ma kotu cewa hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari guda biyu Sha’aban Sharada da Bashir Ibrahim, da kuma Hafiz Ibrahim, sun kai rahoton lamarin ga hedkwatan yan sandan jihar Kano a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Kotu ta dage shari’an da akeyi da mai kwaikwayon Buhari
Kotu ta dage shari’an da akeyi da mai kwaikwayon Buhari

Ekwe ya fada ma kotu cewa a ranar 14 ga watan Janairu, wanda ake karan ya shirya wani shiri agidan radiyon Aminci a Kano, inda ya zagi masu karan uku da gangan tare da bata masu suna sannan ya kirasu da makaryata.

Ya kuma ce mai laifin ya saci fasahar Buhari sannan yayi yunkurin haifar da sabani a cikin APC.

Ya ce hakan ya ci karo da sashi na 392, 399 da kuma 114.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ma ya bi sahun masu ritaya – PDP ga Tinubu

Ekwe yayi kira ga a dage karan domin a bay an sanda daman kammala bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng