Baru ya kalubalance 'yan kasuwa kan kiyaye farashin man fetir

Baru ya kalubalance 'yan kasuwa kan kiyaye farashin man fetir

- Manajan NNPC, Maikanti Baru, ya umurci 'yan kasuwan man fetur da su tabbatu kan kayyadajjen farashin gwamnati

- Ya yi wannan kira me yayin mika lambar yabo ga kamfanin 'BOVAS & Company Limited da bisa sayar da mai kan N145

- Baru ya yabawa kamfanin saboda yadda ta ke saukakawa rayuwan 'yan Najeriya

Manajan Matatan Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mai Kanti Baru, ya umurci 'yan kasuwan man fetur da su tabbatu kan sayar da man fetur a farashin gwamnati na N145 ko wani lita, don saukakawa rayuwan al'ummar Najeriya.

Baru ya umurci 'yan kasuwan Man Fetur da su tabbatu kan farshin N145 na Fetur
Baru ya umurci 'yan kasuwan Man Fetur da su tabbatu kan farshin N145 na Fetur

Baru ya yi wannan umurni ne yayin mika lambar yabo ga Manajar Kamfanin Man Fetur na 'BOVAS & Company Limited' mai suna Misis Victoria A. Samson. NNPC ta ba ta lambar yabo ne bisa kula da jajircewar ta na tabbatar sayar da man fetur kan N143 kowace lita.

KU KARANTA: Gwamnonin da suka gudu Abuja saboda rikicin makiyaya matsorata ne - Minista

Ya ce Kamfanin da Manajar ta sun cancanci lambar yabo saukakawa rayuwan al'umma. Ya yaba da yadda har Kamfanin ke sayar da mai kasa ma da kayyadajjen farshin gwamnati na N145. Don haka ne ya yi kira ga sauran 'yan kasuwa da su yu koyi da hakan.

Ya kuma shaida ma Samson cewa NNPC a shirye ta ke ta ba wa Kamfanin kowace irin gudummuwa don samarwa jama'a man fetur a dukkan gidajen man ta. Ita kuma Samson ta ji dadi matuka da wannan karamci.

Ta kuma mika godiya ga NNPC. Ta kuma kara da cewar kamfanin ya tabbatu da sayar da mai a kayyadajjen farashin gwamnati hatta lokacin tsananin rashi. Ta kuma jaddada cewar za su cigaba da bayar da hadin kai ga NNPC da PPMC don magance matsalar mai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164