Mun kashe sama da Tiriliyan 1.5 wajen gina hanyoyi a kasar nan – Gwamnatin Buhari
- Gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin kawo gyara a Najeriya
- Daga cikin ayyukan da ake yi akwai hanyoyin jirgin kasa da titi
- Haka kuma dai ana shirin babbako da babban kamfanin Ajaokuta
Mun samu labari daga Jaridar The Guardian Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kashe sama da Tiriliyan daya da rabi cikin shekaru biyu rak inji Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Gwamnatin Tarayya ta kashe Tiriliyan 1.6 domin gina manyan hanyoyi da sauran ayyuka a fadin kasar nan. Daga cikin wadanna ayyuka akwai titin jirgin kasa Legas zuwa Kano da kuma hanyar jirgin kasa na Legas zuwa Kalaba.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta san da matsalar talauci a Najeriya
Farfesa Yemi Osinbajo a Jihar Kogi ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari ta kuma saki kudi na gina gadar da ta hada kasashen kudu na Neja. Mataimakin Shugaban kasar yace wannan Gwamnati ta cin ma nasarorin iri-iri daga hawan ta.
Mataimakin Shugaban na Najeriya ya bayyana yadda Gwamnatin APC ta saki Naira Tiriliyan 1.19 ga Gwamnonin Jihohi daga hawan wannan Gwamnatin zuwa karshen bara. Osinbajo yayi albishir da cewa an kusa tada kamfanin Ajaokuta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng