NAFDAC ta garkame gidajen gasa mummuki guda 24 a Borno
- Hukumar Kula da Tsabtan Abinci da Magunguna (NAFDAC), ta kulle gidajen biredi 24 a Jihar Borno
- Shugaban Hukumar na Jihar, Nasiru Mato, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan
- Ya ce an kule gidajen ne saboda rashin lasisi da rashin tsabtace muhalli
Hukumar Kula da Tsabtan Abinci da Magunguna (NAFDAC), reshen Jihar Borno, ta kulle gidajen sana'anta mummuki (biredi) guda 24 a Jihar, cikin gidaje kimanin 300 da a ke da su a Jihar.
Ta yi wannan kulle ne saboda wasu gidajen su na aiki ba tare da lasisi ba, wadan su kuma su na aiki da takardun boge, wadan su kuma saboda rashin tsabtace muhalli.
KU KARANTA: Jihar Ekiti za ta samar da na ta EFCC din
Shugaban Hukumar na Jihar, Nasiru Mato, shi ne ya sanar da manema labarai hakan a ranar Laraba, a Maiduguri, babban birnin Jihar. Ya ce sun fara fafutukar tabbatar da dukkan gidajen su na aiki bisa ka'ida.
A cikin gidajen da a ka kulle akwai Nurul Aini, Nice Bread, D Boss, Save the Nation, Albarka, Ever-Nice, Aljazeera da dai sauran su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng