Dandalin Kannywood: Tijjani Asase ya mika sakon godiyarsa ga masoya bayan annobar da ya faru da shi
Shahrarren jarumin wasan kwaikwayo na Kannywood, Tijjani Asase, ya mika sakon nuna godiyarsa ga yan’uwa da abokan arziki da suka taimaka masa da kayan agaji bayan annobar gobara ta shafi gidansa.
Zaku tuna cewa a daren Asabar, 3 ga watan fabrairu, 2017 ne annobar gobara ta fada gidansa inda yayi asaran dukkan dukiyoyinsa ba tare tsirata da komai ba.
Jarumin ya yi wannan sanarwar mika godiya ne a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa kuma jiga-jigai da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun kai masa ziyara.
A yayin wannan ziyara da suka kai, wasu daga cikin su sun agaza masa da kayan abinci da kudi har da sutura.
KU KARANTA: Akwai makiya dimokradiyya cikin ministocin Buhari - Saraki
Yace: "Salam barkanmu da safiya da mika godiyata ga iyayan gidana da yayyena wa'yan da suka tayani da alhini. wasu a waya wasu hargida wasa harda gudun mawa sutura da abinci wasu harda kudi nagode Allah yabar zumunci amin nagode". ya rubuta a shafin sa na instagram.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng