Wasu 'yan PDP sun kafa sabuwar kungiya, sun lissafo da hanyoyi 6 don gyara Najeriya

Wasu 'yan PDP sun kafa sabuwar kungiya, sun lissafo da hanyoyi 6 don gyara Najeriya

- A cikin kwanakin nan ne wasu yan jam'iyyar PDP su ka kafa wata kungiya da mai suna 'The New Face of Hope'

- Kungiyar ta ce tana da dan takara wanda zai ceto Najeriya daga cikin halin ha'ula'i da kasar ke ciki na rashin tsaro da matsalar tattalin arziki

- Kungiyar kuma ta bayyana akidojin ta guda 6 da zata aiwatar idan takarar nasu ya samu karbuwa

Sabuwar kungiyar da ta bullo daga jam'iyyar PDP wadda ta kira kanta sabuwar mafita ga yan Najeriya a turence 'New Face of Hope' ta lissafo akidoji guda 6 da dan takarar na su zai mayar da hankali a kai gabanin zaben 2019.

Wasu 'yan PDP sun kafa sabuwar kungiya, sun lissafo da hanyoyi 6 don gyara Najeriya
Wasu 'yan PDP sun kafa sabuwar kungiya, sun lissafo da hanyoyi 6 don gyara Najeriya
Asali: Twitter

A sakon da kakakin kungiyar, Imade Ize-Iyamu ya aike wa Legit.ng a ranar Talata 13 ga watan Fabrairu, ya ce kungiyar ta su zata ceto Najeriya daga cikin halin matsin tattalin arziki da ta fada.

KU KARANTA: Shehu Sani ya gayyato wa JAMB masu kama maciji, ya kuma bayar da gudunmawar maganin macijin

Legit.ng ta gano cewa kungiyar ta fitar da dan takarar shugabancin kasa na zaben 2019 kuma zata gabatar da shi ga uwar jam'iyyar ta PDP kafin zaben 2019.

A cikin sakon da ta aike, kungiyar ta koka kan yadda gwamnati mai ci yanzu na APC ke barin al'umma cikin wahalar rayuwa, yunwa, rashin aikin yi da sauransu.

Ga dai hanyoyi shidan da kungiyar ta ce dan takarar na ta zai bi don kawo gyara a Najeriya:

1. Farfado ta tattalin arziki

2. Samar da ingantacen ilimi

3. Habaka kamfanoni da ma'aikatu

4. Habaka fanin gine-gine

5. Tallafawa mata da matasa

6. Inganta al'adu da sauran su

Kungiyar ta bullo ne a lokaci da jam'iyyar PDP ke lalubo dan takarar zaben shugabancin kasa a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164