Gwamann jihar Bauchi ya kaiwa Maikanti Baru ziyara Abuja

Gwamann jihar Bauchi ya kaiwa Maikanti Baru ziyara Abuja

A yau Litinin 12/02/2018, Mai girma Gwamna Mohammed A. Abubakar Esq yakai ziyara wa Babba Manajan Kamfanin Mai ta Kasa(NNPC) GMD. Dr Maikanti Baru a ofishin sa dake Ma'aikatar a Abuja.

Mai girma Gwamna ya bayyana wa manema labarai cewa ya kawo ziyarar ne don karfafa dangantaka dake tsakanin Ma'aikatar da take binciken mai a Jihar Bauchi da Gwamnatin Jihar Bauchi.

Gwamna yace Babba Manajan Darektan Kamfanin ta (NNPC) dan Jihar Bauchi, don haka ya befi tauntsu biyu ne da dutse daya, (yayi zumunta kuma yayi ziyarar aiki). Yace GMD ya bayyana masa nasarorin da suka samu, wadda yanzu haka za'a fara hako mai a rijiyoyi biyar a Karamar Hukumar Alkaleri.

Gwamann jihar Bauchi ya kaiwa Maikanti Baru ziyara Abuja
Gwamann jihar Bauchi ya kaiwa Maikanti Baru ziyara Abuja

Gwamna ya kara da cewa Kamfanin (NNPC) ya kasance a Jihar Bauchi ne bisa umarni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari don binciko da fara tono mai a Jihar ta hanyar amfani da Ilimin fasaha na zamani.

Gwamna ya jaddada karin goyon bayan Gwamnatin sa bisa wannan labari me karfafa gwiwa da ya samu daga bakin Babban Manajan Kamfanin mai ta Kasa (NNPC) don tabbatar da samuwar nasarar tono mai a Jihar Bauchi.

A bangare guda kuwa, ya tabbatar samun hadin kai da goyon baya daga al'ummar da suke zaune a yankunan da ake wannan aiki na bincike da hako mai a Jihar Bauchi wajen gudanar da aikin su cikin "yanci.

KU KARANTA: Hotunan ganawar shugaba Buhari da tsohon shugaba Abdulsalami

A karshe yayi godiya ta musamman ga Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa wannan namijin kokari da yakeyi na ganin Jihar Bauchi ta zamo daya daga cikin Jihohi masu samar da mai a Najeriya.

Ya kuma yi albishir wa Shugaban Kasa cewa baze bashi kunya ba wajen kawo shirye-shirye da tsare-tsare a Jihar Bauchi musamman ganin yadda abubuwan suke zuwa kai tsaye wajen talakawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng