Nigerian news All categories All tags
Shehu Sani ya gayyato wa JAMB masu kama maciji, ya kuma bayar da gudunmawar maganin macijin

Shehu Sani ya gayyato wa JAMB masu kama maciji, ya kuma bayar da gudunmawar maganin macijin

- Shehu Sani, Sanata mai walkiltar Kaduna ta Tsakiya, ya bayar da mafita game da bacewan kudi a JAMB

- Sanatan ya gayayato wa JAMB ma su kama maciji da ya kuma bayar da maganjn maciji

- Mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, ya ce 'yan Najeriya su daina daukan lamarin kamar wasahi

Ma'aikatan Cibiyar Shirya Jarabawan shiga makarantun gaba da Sakandire (JAMB) sun sha mamaki a safiyar Talata yayin da Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta Tsakiya ya shigo ofishin na su dauke da maganin maciji da kuma masu kama maciji bayan wata ma'aikaciyar hukumar tayi ikirarin cewa maciji ta hadiye N36m.

Shehu Sani ya ziyarci hukumar JAMB, ya bayar da tallafin maganin maciji

Shehu Sani ya ziyarci hukumar JAMB, ya bayar da tallafin maganin maciji

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya sha dariya a lokacin da Sanata Shehu Sani ya mika masa kwalaye buyu na maganin maciji ya kuma ce ya zo tare da mai kama macizai guda biyu don su taimaka wajen nemo macijin da ya hadiye kudaden.

Daya daga cikin masu kama macijin, Tasiu Abdulrasheed wanda ya ce a tsawon shekaru 20 da ya yi yana sana'ar kama maciji bai daba karo da maciji mai hadiye kudi ba.

KU KARANTA: Kotu ta daure mutane biyu da su ka yi sata a coci

Sanatan ya kuma ce idan har maciji zai hadiye irin wannan makudan kudi to lallai za a wayi gari maciji washe asusun Kasar gaba daya, ya yi ma sa karkatakaf.

Shi kuwa mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, cewa ya yi abun takaici ne yadda 'yan Najeriya su ka dauki abun kamar wasa. A cewar sa, abu ne da ya kamata a ce kowani dan Najeriya ya yi jimamin faruwar hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel