Babu jami'an 'yan sanda cikin mata 10 da ake ceto daga hannun Boko Haram - Rundunar 'Yansanda

Babu jami'an 'yan sanda cikin mata 10 da ake ceto daga hannun Boko Haram - Rundunar 'Yansanda

- Kwashinan Yan Sanda ya karyata rahotanin da ke yaduwa wanda ke cewa mata 10 da aka ceto daga hannun Boko Haram jami'an yan sanda ne

- Mista Damian Chukwuma ya ce mata 10 da aka ceto mazauna jihar Borno ne wanda aka sace a tsakanin watanin Yuni da Yulin 2017 amma basu da wata alaka da rundunar yan sanda

- Chukwuma ya kara da cewa jami'an yan sanda daya ne tak aka sace a harin da Boko Haram suka kai 20 ga watan Yulin 2017 a hanyar su ta zuwa jana'iza a garin Lassa

Kwamishinan Rundunar Yan sanda na jihar Borno, Mista Damian Chukwu ya ce mata goma da aka ceto daga hannun mayakan Boko Haram ba jami'an yan sanda bane kuma ba matan jami'an yan sanda bane.

Chukwu ya ce mutane 13 aka ceto, 3 daga cikin su ma'aikatan jamia'r tarayya na Maiduguri ne, sauran 10 kuma mata ne da kungiyar ta Boko Haram suka sace a samamen da suka kaiwa tsakanin watan Yuni da Yulin 2017.

Mata 10 da ake ceto daga hannun Boko Haram ta jami'an 'yan sanda bane
Mata 10 da ake ceto daga hannun Boko Haram ta jami'an 'yan sanda bane

Chukwu ya yi wannan bayanin ne a yayin da yake yiwa manema labarai bayani a taron wata-wata na rundunar a ranar Litini a Maiduguri.

KU KARANTA: Zaben 2019: Ka koma gida ka hutu, Junaid ya fadawa shugaba Buhari

Ya karyata rahoton da ke yaduwa a wasu kafafen labarai wanda ke cewa 10 daga cikin mutane 13 da ake ceto daga Boko Haram jami'an rundunar Yan sandan ne.

A sokon muryar da kamfanin dillancin labarai (NAN) ta samar, Chukwu ya ce: " Rahotnin da ake yadawa ba gaskiya bane. Idan ba'a manta ba a ranar 20 ga watan Yulin 2017 , mayakan Boko Haram su kai hari ga wata tawagar mutane da ke hanyar su na zuwa garin Lassa da ke karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno.

"A harin ne yan Boko Haram din suka kwace babbar motar da ke dauke da mutane, wasu daga cikin mutanen sun gudu cikin daji amma Boko Haram sun tafi da wasu daga cikin su.

"Cikin wanda ake tafi da su din akwai Jami'ar Yan sanda guda daya wadda ke aiki da sashin binciken manyan laifuka CIB wadda kawa ce ga jami'an da ta rasu, bayan ita sauran matan da aka sace basu da wata alaka da rundunar yan sanda ko iyalan su."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: