Gwamnatin tarayya ta kashe $6.4 billion a yankin Arewa maso gabas cikin shekaru 2 - Minista Zainab Shamsuna

Gwamnatin tarayya ta kashe $6.4 billion a yankin Arewa maso gabas cikin shekaru 2 - Minista Zainab Shamsuna

Karamar ministan kasafin kudi, Zainab Ahmed Sahmsuna, ta bayyana ranan Alhamis cewa gwamnatin tarayya da jihohin yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun kashe $6.4 billion a yankin tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

Ministar ta bayyana hakan ne a taron kaddamar da shirin bayar da agaji domin yankin Arewa maso gabas a Abuja.

Ta kara da cewa an shirya taron bisa ga hadakar shugaba Muhammadu Buhari ta kuma kwamitin majalisar dinkin duniya.

Gwamnatin tarayya ta kashe $6.4 billion a yankin Arewa maso gabas cikin shekaru 2 - Minista Zainab Shamsuna
Gwamnatin tarayya ta kashe $6.4 billion a yankin Arewa maso gabas cikin shekaru 2 - Minista Zainab Shamsuna

Game da cewarta, an kashe $3.3bn a 2016 kuma $3.1bn a 2017. Kana kuma a 2018, anyi kasafin irin wannan kudin.

Ta bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya zata bada gudunmuwa ga shirin. Ta mika godiyanta ga dukkan masu bayar da agaji daga kasashen waje domin ceton rayukan jama’a Arewa maso gabas.

KU KARANTA: Kada jawabin Shekau ya yaudareku, suna shirin kai sabbin hare-hare ne - Ahmed Salkida

Tana cigaba da mika kokon bararta ga al’umma saboda a cimma taimakawa mutane 7.7 million masu neman taimako a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng