Mutane da dama sun rasu sakamakon sabon rikicin da ya barke a Adamawa
- Rikicin kabilu a Jihar Adamawa ya ki ci ya ki cinyewa
- A na tsammanin mutane 6 ne su ka rasu a sabon yamutsi tsakanin kabilu a Jihar
- An baza Soji da 'Yansanda a Jihar don tabbatar da tsaro da zaman lafiya
A na tsammanin mutane da dama sun rasa rayukan su sakamakon rikicin kabilu a Gundumar Libbo ta Karamar Hukumar Shellenge ta Jihar Adamawa. Kansilan Gundumar, Shu'aibu Waleed, ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), da barkewar rikicin.
Waleed ya ce rikicin ya barke ne sakamakon gawan wani mutum da a ka gani dan shiyyar Gomba na Karamar Hukumar Demsa wacce ta ke makotaka da Shellenge.
Mutanen Gomba sai su ka yi zargin makiyaya ne su ka kashe shi.
Daga baya sai a ka ga gawawwakin makiyaya guda 2 wanda a ka sakankance kisan ramuwa ne a ka ma su.
KARANTA KUMA: EFCC za ta kara bankado bincike a kan tsaffin gwamnoni 14
Waheed bai iya bayar da adadin mutanen da su ka rasu ba. Sai dai ya ce sun binne mutuane 5 an kuma ga gawa 1 da a ka kone kurmus. An kuma kone kimanin gidaje 200.
Sakataren Gudanarwa na Hukumar Bayar Tallafin Gaggawa na Jihar (ADEMSA), mai suna Mista Abubakar Furo, ya shaida cewar kabilu 6 ne wannan rikici ya shafa. Sai dai kuma an baza jami'an tsaro, har zaman lafiya ya fara dawowa a yankunan.
Mai magana da yawun Hukumar 'Yansanda na Jihar, SP Abubakar Usman, ya tabbatar da baza jami'an tsaro da kuma dawowar c c c lafiya. Sai dai Shi ma bai san adadin rayukan da a ka rasa ba tukunna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng