Gwamnatin jihar Ebonyi ta umurci masu sarautun gargajiya su samar wa makiyaya filayen kiwo

Gwamnatin jihar Ebonyi ta umurci masu sarautun gargajiya su samar wa makiyaya filayen kiwo

- Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya bayar da umurnin tanadar wa makiyaya filayen da za su rika kiwo a jihar

- Umahi ya ce an cin ma wannan matsayan ne bayan tattaunawa da ya yi tsakanin hukumomin tsaro da wakilan makiyaya da kuma manoma

- Gwamnan ya ce duk wanda aka samu ya kashe shanu ko kuma barnata amfanin gona zai fuskanci hukunci mai tsanani

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya umurci masu sarautun gargajiya a ta Ebonyi su tattaro bayan game da makiyayan da ke kiwo a jihar domin a tanadar masu filayen kiwo don hakan ne zai samar da zaman lafiya.

Umahi ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Juma'a waje wani taro da ya yi da masu sarautun gargajiya da kuma masu hakar ma'adinai a jihar ranar Juma'a, bayanan sun hada da sunayen makiyayan, inda suke zaune da kuma lambobin wayar salular su.

Gwamnatin jihar Ebonyi ta umurci masu sarautun gargagjiya su samar wa makiyaya fiayen kiwo
Gwamnatin jihar Ebonyi ta umurci masu sarautun gargagjiya su samar wa makiyaya fiayen kiwo

A cewar Gwamna, a cin ma wannan matsayan ne bayan taruka da ya yi da hukumomin tsaro da kuma wakilan kungiyoyin makiyaya da dama a jihar.

KU KARANTA: Rayuwa ta na cikin hadari, inji mai magana da yawun Babangida, Afegbua

Umahi ya yi kira ga masu sarautun gargajiyan su bayar da hadin kai ga shirin domin hakan ne zai tabbatar da zaman lafiyar da aka dade ana mora tsakanin makiyaya da al'ummar jihar.

Ya kuma ce zai samar da ruwa ga makiyayan a inda za su rika kiwon don a halin yanzu jihar sa ba ta da kudin gina filin kiwo na zamani, ya kara da cewa makiyayan za su rika canja wuri idan ciyawar da dabobin su ke amfani da shi ya kare.

Gwamna kuma ya yi gargadin cewa duk wanda ya kashe shanu za'a rubunya masa kudin sau biyu ya biya, hakazalika, duk makiyayin da ya barnata amfanin gona, za'a tilasta masa barin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164