Son zaman lafiya da kuma bin umurnin shugabanin kasa yasa Kwankwaso dakatar da ziyarar sa - Dan majalisa, Abubakar Nuhu
Wani jigo a kingiyar Kwankwasiya Wanda Kuma shine Dan majalisar wakilai na mazabar Kano ta tsakiya,Alhaji Abubakar Nuhu Dan Buram yace ,bin umurnin shugabanin da kuma gudun zubar da jini yasa jagoran su sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya janye ziyarar da aka shirya zai Kai Kano a yan kwanakin baya Amma ba wai tsoro ba,kamar yadda manyan Jami,an gwanatin jihar Kano suke ta fada.
Alhaji Abubakar Nuhu Wanda tsohon kwamishinan kudi ne a tsohuwar gwanatin jihar yace Sanata Kwankwaso Mai son zaman lafiya ne Kuma bazai taba yarda a zubar da jini akan Shi ba,saboda siyasa ba hauka bane.
mun samu labarin irin mugun shirya da gwanatin Gunduje tayi wajen tattaro yan Sara Suka domin su farma magoya bayan mu ga Kuma gargadin da kwamishinan Yan sanda jihar yayi,sai Kuma Kira da fadar shugaban kasa tayi mana,hakan ya sa muka yanke shawarar janye ziyarar Amma ba don tsoro ba.
Dan majalisar yace babu yadda yadda yadda,za ayi a hana zababben sanata damar shiga mazabar sa domin ganawa da mutanin da Suka zabe Shi.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabbin jakadu 3
Abubakar Nuhu Dan Buram ya bukaci magoya bayan Kwankwaso a duk inda suke da su kasance masu son zaman lafiya domin sai da zaman lafiya za,a samu ci gaban kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng