Abin tausayi, 'yan gida daya mutum shida ne suka rasu a hadarin mota a Bauchi
- Wani mummunan hatsari ya faru a kauyen Buzaye da ke garin Bauchi inda mutane shida yan gida daya suka rasu
- Hadarin ya faru ne sakamakon karo da motar da iyalan ke ciki tayi da wata tipa mara fitila a daren jiya Laraba
- Jami'an hukumar kare haddura na kasa sun garzaya wajen da abin ya faru kuma sun kai gawawakin zuwa Asibiti
Mutune shida dukkan su yan gida daya ne suka rasa rayyukansu sakamakon wani mumunan hadarin mota da ya faru a kauyen Buzaye da ke karamar hukumar Bauchi na jihar ta Bauchi yayin da suke dawowa daga wata tafiya da sukayi.
Shugaban gudanarwa na Hukumar Kiyaye Hadura na Kasa (FRSC), Paul Gua ne ya bayar da sanarwan inda ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe tara na daren jiya a kauyen Buzaye.
KU KARANTA: Gwamna Bindow zai dora mashawarta 20 daga ma'aikatan tasha
Kamar yadda ya bayyana, hatsarin ya faru ne sakamakon karo da motar da iyalan suke ciki mai kirar Honda Civic tayi da wata babban motar tipa da fitilar ta ke da matsala.
Ya kuma ce bayan jami'an hukumar sun sami labarin afkuwar lamarin, sun garzaya wajen da hatsarin ya faru kuma sun kwashe gawawakin sun kai Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ABUTH) da ke Bauchi
A wani rahoton kuma Legit.ng ta ruwaito labarin da Yan Sandan jihar Ondo suka ceto wasu muaten uku daga hannun yan fashi da sukayi garkuwa da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng