An farfado da tashan jiragen ruwa na Ikorodu
- Hukumar Kula da Tashohin Jiragen Ruwa (NPA) ta kaddamar da fara jigilar kayayaki daga tashar Ikorodu zuwa tashar jirgin ruwa na Legas
- Shugaban hukumar, Hadiza Bala Usman ta ce farfado da tashar zai saukaka cinkoso da ake samu a tashar Legas kuma zai bunkasa kasuwanci da tattalin arzikin kasa
- Hadiza Bala Usman kuma tayi kira ga manoma da sauran yan kasuwa su garzayo domin amfana da garabasar sayar da kayayakin su a kasuwanin duniya
Hukumar Kula da Tashohin Jiragen Ruwa na Kasa (NPA) ta fara jigilar amfanin gona daga tashan jiragen ruwa na Ikorodu zuwa kasashen ketare. Kamar yadda NPA ta bayyana, fara jigilar zai sawake cinkoso da ake fama dashi a tashar Legas kuma ya bunkasa kasuwanci.
A jawabin da tayi yayin kaddamar ta fara jigilar kayan daga tashar Ikorodu zuwa tashar Legas, Shugaban Hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta ce Hukumar na ta ne ke da hakkin cewa anyi amfani da tashar ta Ikorodu ta hanyar da ya dace domin yan Najeriya su amfana.
KU KARANTA: NNPC ta afkawa 'yan bunburutu da 'yan kasuwan man fetur
Ta cigaba da cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankali sosai wajen tallafa wa yan Najeriya masu son fita da kayayakin noma zuwa kasashen Ketare, sannan Hukumar ta NPA za ta tabbatar an bi hanyoyin da suka dace wajen saukaka ma yan kasuwa da manoman.
Tayi kira ga yan Najeriya su fito su amfana da wannan garabasar na sayar da amfanin gonar su a kasuwanin duniya wanda hakan zai bunkasa tatallin arzikin Najeriya sosai.
Yan kasuwa da manoma da suka hallarci kaddamar da fara jigilar kayayaki a tashan sun bayyana farin cikin su bisa yadda Gwamnati ta farfado da tashar.
A wani labarin kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa Hukumar ta kula da tashoshin jiragen ruwa NPA ta samar da kudin shiga wanda ya kai naira billiyon 299.5 a shekarar 2017 da ya gabata kamar yadda Abdullahi Goje ya bayyana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng