Da gurbatattun ‘Yan Kannywood na ke rikici ba da Ali Nuhu ba - Adam Zango

Da gurbatattun ‘Yan Kannywood na ke rikici ba da Ali Nuhu ba - Adam Zango

Shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan hausa Adam A. Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana cewa shi ba da sarki mai Kannywood wato Ali Nuhu yake rigima ba kamar yadda wasu mutane ke zata.

Jarumin wanda ya yi tashe a wani sabon fim nasa mai suna “Gwaska Returns” yana mai koke wajen kwato hakkin sauran abokan aikinsa.

Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram inda ya caccaki gurbatatun yan kannywood masu ruwa da tsaki akan miyagun ayyukan da suke yi na rashin adalci da kuma bayar da cikakakken hakkin jama’ a.

Da gurbatattun ‘Yan Kannywood na ke rikici ba da Ali Nuhu ba - Adam Zango
Da gurbatattun ‘Yan Kannywood na ke rikici ba da Ali Nuhu ba - Adam Zango

Yace kofa a bude yake ga masu neman hada hannu wajen neman hakkinsu domin a yanzu shi kadai ne a cikinta.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Benuwe: Sufetan ‘Yan Sanda ba da gaske yake ba inji wata Kungiya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shahararren tauraron nan na fina-finan Hausa Rabi'u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya ce aikin soja ya fi fim sauki.

A cewar jarumin idan mutun na fitowa a matsayin jarumi baya samun lokaci na kansa da zai ce harma zai hada fim nasa na kansa.

Inda ya jaddada cewa harkar fim ya fi na soja wahala domin su sojoji akan samu ranar da suke hutu basa kan aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng