NNPC ta afkawa 'yan bunburutu da 'yan kasuwan man fetur
- Matatan Man Fetur na Najeriya (NNPC), ta tsananta farautar 'yan bunburutu da 'yan kasuwan mai ma su laifi
- Ta kama manajojin gidajen mai guda 2 da laifin karkatar da lita 66,000 na man fetur
- Za a ci su taran N250 a kowace lita 1 na mai da su ka karkatar
A ranar Laraba ne Matatan Man Fetur na Najeriya (NNPC), ta bayyana cewar ta tsananta kame da hukunta 'yan kasuwan man fetur ma su laifi da 'yan bunburutu a fadin Kasar nan.
Mai magana da yawun NNPC, Mista Ndu Ughamadu, ne ya bayyana hakan a Abuja, a inda ya ce a na hakan ne don tsabtace harkar sayar da man fetur da kuma kawar da matsanancin layi da a ke samu a gidajen mai.
Ya ce an kama 'yan bunburutu guda 6 da manajoji guda biyu na gidajen mai, da laifin karkatar da man fetur lita 66,000. Za a ci su taran N250 a kowani lita 1.
KU KARANTA: Yaki da Boko Haram: Hukumar Soji ta yi wa Shettima raddi
Su kuma 'yan bunburutun Alkali ya yanke ma su zaman gidan yari na watanni 2 ko biyan tara na N2,000, a inda nan take su ka biya. Mun samu wannan labari ne daga kamfanin Dillancin Labarai (NAN).
A wata labarin kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa Hukumae DPR ta garkame gidajen man fetur uku a garin a Miaduguri saboda sabawa dokar gwamnati da kuma zambattar masu sayaya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng