Zamfara ta karyata rahoton da ya nuna dalibai 24 kadai suka ci jarrabawar NECO

Zamfara ta karyata rahoton da ya nuna dalibai 24 kadai suka ci jarrabawar NECO

- Gwamnatin jihar Zamfara ta ce dalibai 11,000 suka ci jarabwar NECO

- Kwamishinan jihar Zamfara ya ce makiyan jhar Zamfara suke yada labarin karya akan jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta karyata rahoton da ya nuna dalibai 24 kadai suka ci jarabawar NECO a jihar

Kwamishinan ilimi na jihar Zamfara, Muntaka Rini, ya fadawa manema labaru cewa makiyan jihar ne suka kago labarin karya suka dangantashi da jihar Zamfara.

KU KARANTA : Hukumar NPA ta samar da kudaden shiga Naira biliyan N299.5 a shekara 2017

Muntaka Rini yace, labarin ya fusata ma’aikatan ilimi jihar Zamfara da mutanen jihar.

Zamfara ta karyata rahoton da ya nuna dalibai 24 kadai suka ci jarrabawar NECO
Zamfara ta karyata rahoton da ya nuna dalibai 24 kadai suka ci jarrabawar NECO

Rini, yace bayan jarabawan NECO da 'yan sakandare suke rubutawa a fadin kasar, akwai wani jarabawa na musaman da hukumar NECO ke gudanarwa wanda ba kowa ke rubutawa ba (GCE ) shine wanda dalibai 24 daga jihar Zamfara suka yi nasara.

Amma kafofin watsa labaru da ‘yan jaridu sun kasa tantance wannan labarin. Rini ya ce dalibai 11, 000 suka saka ci jarabawar NECO a jihar Zamfara daga cikin dalibai 24,000 da suka rubuta. jarabawan

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng