Sanata Shehu Sani ya tada jijiyar wuya a majalisa bisa watsi da aka yi da mutanen aka kai ma hari a Birnin Gwari

Sanata Shehu Sani ya tada jijiyar wuya a majalisa bisa watsi da aka yi da mutanen aka kai ma hari a Birnin Gwari

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya nuna damuwarsa da hare haren da ake yawan samu a mazabarsa, yankin karamar hukumar Birnin Gwari, inda ya ce bai dace a wancakalar da mutanen da abin ya shafa ba.

Sani ya bayyana haka ne a zaman majalisa na ranar Talata 6 ga watan Feburairu, inda ya zargi gwamnati da kuma hukumomin tsaron gwamnatin da nuna halin rashin damuwa da ayyukan yan bindigan a jihar Kaduna, inji rahoton Premium Times.

KU KARANTA: Yaron Dahiru Bauchi ya kafirta duk wanda yace Shehu Tijjani Allah ne

Sanatan ya bayyana ma majalisar dattawa cewa ayyukan sace sacen mutane, fashi da Makai da garkuwa da mutane ya zama ruwna dare a jihar Kaduna, amma duk da haka gwmnatin tarayya bata nuna damuwarta na magance matsalar ba.

Sanata Shehu Sani ya tada jijiyar wuya a majalisa bisa watsi da aka yi da mutanen aka kai ma hari a Birnin Gwari
Sanata Shehu Sani ya tada jijiyar wuya a majalisa bisa watsi da aka yi da mutanen aka kai ma hari a Birnin Gwari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana fadin “Na damu kwarai da gaske da yadda gwamnatin tarayya bata iya tabbatar da tsaron yan Najeriya, balle mana dukiyoyinsum gwamnati ta gaza.

“Abin kunya ne ace bayan sama da shekaru 100 da samar da Najeriya amma yan Najeriya basa iya zama cikin tsaro a kasarsu, amma kasashen Kamaru, Nijar da Bini duk suna da ingantaccen tsaro. Don haka ina kira ga duk wanda lamarin ya shafa da su mayar da hankalinsu kan matsalar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwmanatin jihar Benuwe ta sanya naira miliyan 50 a matsayin ladan da zata baiwa duk wanda ya kai mata tsegumin inda wani shahararren dan ta’adda mai suna Ghana yake, wanda ake zargi da kai hare hare a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng