Aliko Dangote ya horas da matasa da dama a Kasar Indiya

Aliko Dangote ya horas da matasa da dama a Kasar Indiya

- An tura mutane 150 domin su san kai aiki daga Kamfanin Dangote

- Yanzu haka Matasa da dama sun samu horo sosai a kasar Indiya

- Ana sa rai matatar Dangote ta samawa mutane sama da 4000 aiki

Mun samu labari cewa Dangote ya horas da mutane 150 a kasar waje domin shiryawa katafaren kamfanin Dangote da za a bude na tace danyen man fetur nan gaba a Garin Legas. Kamfanin zai samawa ‘Yan Najeriya aiki kuma ya sa a rage shigo da kayan waje.

Aliko Dangote ya horas da matasa 150 a Kasar Indiya
Ana shirin kammala aikin matatar Dangote a Legas

Mohan Kumar wanda shi ne Darektan kamfanin wajen abin da ya shafi sha’anin ma’aikata ya bayyana cewa sun horar da jama’a domin sanin kan aiki a Kamfanin na Dangote yayin yake kaddamar da wasu Injiniyoyi da su ka dawo daga waje kwanan nan.

KU KARANTA: Mutanen Jihar Neja sun yaba da Gwamnatin Buhari

Mista Kumar ya bayyana cewa an yi wa wasu matasa 22 horo a kasar Indiya domin koyon yadda ake aiki a matarar danyen mai daga kwararru. Wan horar da matasan ne domin su koyi yadda ake tace danyan mai kafin a fara aiki a babban kamfanin na Dangote.

Yanzu haka dai an horar da mutane 150 a hannun kwararru a Indiya kuma ana sa rai za a kara aika wasu 600 zuwa kasar kafin karshen watan Afrilu. Dama ku na da labari Dangote zai fara tace man fetur da kuma hada taki kwanan nan a Najeriya inda jama’a za su karu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng