Ababe 9 dake janyo warin baki tare da hanyoyin ƙaurace musu

Ababe 9 dake janyo warin baki tare da hanyoyin ƙaurace musu

Cikin kowane lungu da saƙo na fadin duniya, cutar warin baki wanda a turance ake mata Halitosis, ta kan jefa mai fama da ita cikin damuwa a kullum, ta yadda ba ya iya samun kwanciyar hankali na shiga da kuma mu'amala tare mutane.

Warin baki
Warin baki

Shi dai warin baki abu ne dake jefa mai fama da shi cikin tasku na rashin walwala da kuma damuwa a koda yaushe, sai dai ba bu wanda yafi ƙarfin wannan cuta domin kuwa ta na iya kama kowa.

Bincike da sanadin jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hasashe ya gano cewar akwai mutum daya cikin hudu dake fama da warin baki a kowane yanayi na rayuwa.

Jaridar ta kawo jerin ababe dake janyo warin baki da suka hadar:

1. Sigari

2. Abinci dake maƙalewa a tsakankanin hakori.

3. Rashin gudanar yawu a cikin baki.

4. Rashin cin abinci da ƙarancin sunadaran carbohydrates a jikin mutum.

5. Magunguna: Akwai magungunan da amfani da su sukan janyo warin baki ta hanyar taƙaita gudanar yawun baka.

6. Cutar daji da kuma hanta.

7. Ciwon baki, hanci da maƙoshi

8. Akwai ciwon cikin da yake gadar da warin baki.

9. Mura da tari mai tsananin gaske, wadda a turance ake ce da ita Pneumonia.

KARANTA KUMA: Illoli 6 na lemun tsami ga lafiyar ɗan Adam

Hanyoyin ƙauracewa cutar ciwon baki:

1. Yin burushi ko asuwaki kamar sau biyu a rana.

2. Sauya burushi ko asuwaki duk bayan watanni biyu zuwa uku.

3. Tabbatar da tsaftar abinci kafin a sanya a baki

4. Rage amfani da nau'ikan abinci masu sanya warin baki kamar albasa, tafarnuwa, barasa da sauransu.

5. Yawan shan ruwa da zai ƙara arzikin yawun baka.

6. Kauracewa sigari da dangin ta.

7. Kauracewa shan kayan zaƙi kafin kwanciyar bacci.

8. Lizintar kurkurar baki lokaci bayan lokaci da dumamen ruwa mai gishiri a cikin sa.

A baya kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda rage nauyi tare da tebar jiki ke da tasiri a bangarorin lafiya na dan Adam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel