Karfin wutan lantarki zai karu bana a Najeriya - Fashola
- Ana sa rai wuta zai gyaru zuwa karshen bana a Najeriya
- Akwai ayyukan da ake shirin kamallawa da dama a kasar
- Bayan nan kuma akwai wasu ayyukan wutan da aka yi nisa
Bisa dukkan alamu karfin wutan lantarki zai karu bana a Najeriya kamar yadda Fadar Shugaban kasa ta bayyana. A shekarar nan an sa rai a gama wasu ayyukan wuta da ake yi a fadin kasar wanda kuma za ayi nisa a wadanda ke kasa da ake yi a wasu wuraren.
Mnistan wuta na kasar Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa a na sa rai a shekarar nan a kammala aikin tashar wutar da ke Azura da kuma wani aiki da ake yi a Katsina inda za ayi amfani da karfin iska. Haka nan kuma akwai wasu ayyukanwuta a Kaduna.
KU KARANTA: Kashe-ksshen da ake yi a kasar nan yayi yawa - Shehu Sani
Bayan nan, Fashola ya bayyana cewa za a karasa aikin Gurara da kuma na Dadin Kowa da aikin tashar Kashimbilla. Haka-zalika akwai aikin da yanzu ya kusa zuwa karshe da ake yi a Gbarain da kuma wani gagarumin aiki da ake daf da karewa a Afam.
Idan dai aka kammala wadannan aiki za a samu karin mega watts sama da 1000 a kasar wanda hakan zai taimakawa wajen karfin wuta. Kwanaki Kamfanin wutan Najeriya ya samu sama da Megawatt na wuta 5,222 wanda hakan ba kasafai bane a Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng