An maida Najeriya wajen zubar da jinin Bil Adama inji Sanata Shehu Sani
- Wani Sanatan APC ya koka da yadda ake kashe Jama’a kullum
- Shehu Sani ya nuna abin da ke faruwa na nema ya zama hauka
- ‘Dan Majalisar yace sauraran kasashe ba a samun wannan ta’asa
Labari ya zo mana cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani a Majalisar Dattawa ya koka da yadda aka maida kasar Najeriya wajen zubar da jinin Bil Adama safe, rana, da kuma dare.
Sanata Shehu Sani da ke wakiltar Jihar Kaduna a Majalisa yayi amfani da shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita yayi tir da yadda ake barnar jinanen Bayin Allah da ba su ci ba kuma ba su sha ba cikin kwanakin nan a Najeriya.
KU KARANTA: Babangida Aliyu zai zama Shugaban kasa a 2019
Shehu Sani yake cewa a wasu kasashen akan samu irin wannan masifar ne sau daya kurum. A Najeriya dai har wa yau, wannan abu ya ki ci, ya kuma ki cinyewa. Kwamared Shehu Sani yace har yada hotunan ta’asar ake yi a kafafen labarai.
Kwamared Sani yana martani ne game da abin da ke faruwa a Yankin Benuwe da irin su Filato da kudancin Kaduna da ake ta fama da barna iri-iri wanda har yau ba a ga karshen sa ba. Kwanan nan ma wani Sanatan PDP ya caccaki Gwamnatin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng