Siyasar Kano: Manyan kasa na kokarin sasanta Kwankwaso da Ganduje

Siyasar Kano: Manyan kasa na kokarin sasanta Kwankwaso da Ganduje

Rahotanni sun kawo cewa wasu manyan kasa na yunkurin ganin sun sasanta rikicin dake tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kamar yadda kuka sani baraka ta shiga tsakanin aminan guda biyu tun bayan kammala zaben 2015.

Hasasahen masana harkokin siyasa sun nuna cewa kokarin da Kwankwaso yayi wajen sanya baki cikin al’amuran gwamnatin Ganduje ne ya kawo rabuwar aki a tsakaninsu, koda dai bangaren Kwankwaso ya sha karyata wannan zargi.

Siyasar Kano: Manyan kasa na kokarin sasanta Kwankwaso da Ganduje
Siyasar Kano: Manyan kasa na kokarin sasanta Kwankwaso da Ganduje

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa BBC cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne a kan gaba wurin sasanta ‘yan siyasar biyu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Babban sakataren kungiyar Anglican ya isa fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Buhari

Majiyar dai ta ce ganawar da tsohon gwamnan ya yi da mataimakin shugaban kasa a lokacin da ake tsaka da rudani kan batun shirin kai ziyararsa jihar ta Kano ce ta yaye labulen yin sulhu tsakanin bangarorin biyu.

A kuma ziyarar da mataimakin shugaban kasa ya kai Kano a karshen makon jiya, ya gana da Gwamna Ganduje domin ci gaba da sulhu tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai-ci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng