Wata babbar kotun Abuja zata cigaba da sauraron karar Maryam Sanda a yau

Wata babbar kotun Abuja zata cigaba da sauraron karar Maryam Sanda a yau

- Ana tuhumar Maryam Sanda da kashe mijinta, Bilyamin Muhammed Bello, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello

- An fara gurfanar da Maryam Sanda gaban kotu a watan Disamba bayan hukumar 'yan sanda ta sameta da laifin kashe mijinta ta hanyar caccaka masa wuka

- Bayan Maryam da ragowar wadanda ake kara sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da shi, kotu ta tsayar da yau, 5 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraron karar

Wata babbar kotun Abuja zata fara sauraron karar da hukumar 'yan sanda ta shigar da Maryam Sanda bayan ta tabbatar da cewar ta sameta da laifin kashe mijinta, Bilyamin Muhammed Bello, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Halliru Bello.

An fara gurfanar da Maryam gaban kotu a watan Disambar shekarar da ta gabata, 2017, ana tuhumar ta da kashe mijinta, ta hanyar caccaka masa wuka, a watan Nuwambar 2017.

An gurfanar da mahaifiyar Maryam, Maimuna Aliyu, da dan uwanta, Aliyu Sanda, bisa zarginsu da kokarin boye shaidar kisan da Maryam ta aikata.

Kotun zata cigaba da sauraron karar Maryam Sanda a yau
Maryam Sanda

A daya daga cikin tuhumar da hukumar 'yan sanda ke yiwa Maryam dangane da kisan Bilyamin ita ce, "kin soki mijinki da wuka a kirji da wasu sassan jikinsa da wasu makamai masu hatsari har hakan ta kai ga mutuwar sa."

DUBA WANNAN: Har da wani Limami cikin garada 9 da suka yiwa 'yar shekara 13 fyade har tayi ciki

Tuhuma ta biyu ita ce ta zargin mahaifiyar Maryam, Maimuna da dan uwanta Aliyu, da masaniyar aikata kisan kai tare da kokarin boye shaidar da hukuma kan iya kafa hujja da su, domin tserar da Maryam daga fuskantar hukunci.

Dukkan wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake masu. Kotun ta bayar da umarnin cigaba da tsare Maryam yayin da ta saki Mahaifiyar ta da uwanta a kan beli.

Kotun ta daga cigaba da sauraron karar ya zuwa yau, 5 ga watan Fabrairu, 2018.

Legit.ng ta kawo maku rahotanni masu yawa dangane da badakalar kisan Bilyamin da ake zargin matar sa, Maryam, da aikatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: