Mai duba lafiyar matar Shekau ta saduda, ta mika wuya ga jami'an tsaro
- Mai duba lafiyar matar shugaban kungiyar Boko Haram ta mika wuya ga jami'an tsaro ranar Asabar
- Kwamandan rundunar Ofireshon Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas, ne ya tabbatar da hakan
- Likitar ta bayyana cewar Shekau ne da kansa ke duba lafiyar mayakan kungiyar Boko Haram
Rabi Abu-Yasir, mai duba lafiyar matar shugaban kungiyar Boko Haram, ta mika wuya ga jami'an tsaron Najeriya a jiya asabar.
Kwamandan rundunar Ofireshon Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas, ya tabbatar da hakan yayin mika mutane fiye da 82 da su ka kubutar daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram ga hukumar bayar da agajin gaggawa (SEMA) a jihar Maiduguri.
Rabi ta sanar da manema labarai cewar Shekau ne da kansa ke duba lafiyar mayakan kungiyar Boko Haram tare da bayyana cewar an kubutar da ita tare da ragowar mutanen ne daga hannun kungiyar a dajin Sambisa.
Da take bayar da labarin rayuwar ta a hannun kungiyar Boko Haram, Rabi, ta ce ta samu karramawa daga wurin mayakan kungiyar saboda yanayin aikin da take yi.
DUBA WANNAN: Rundunar soji ta yi wa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe da dama
"Mijina Abu-Yasr likitan Shekau ne, yana duba lafiyar mayakan kungiyar domin har tiyata yake yi masu," inji Rabi.
Ta kara da cewar "Abincin da su ke bani daban yake da na ragowar. Sun tsoratar da mu cewar sojojin Najeriya za su kashe duk ya mika wuya, a saboda haka su ka bukaci mu cigaba da zama da su domin tsira da rayukan mu amma yanzu bayan mun mika wuya, mun gane cewar ba gaskiya suka fada mana ba."
Manjo Nicholas ya ce sun tserar da mutanen ne bayan ragargazar mayakan kungiyar Boko Haram. Sannan ya yi kira ga ragowar mayakan kungiyar da har yanzu ke boye a dajin Sambisa da su fito su mika wuya.
A ranar Juma'a da ta gabata ne jaridar Legit.ng ta kawo maku labarin cewar kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 86 ne suka mika wuya ga jami'an tsaro a jihar Borno.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng