Illoli 6 na lemun tsami ga lafiyar ɗan Adam
Duk da irin amfani na lemun tsamiya ga lafiyar ɗan Adam, yana kuma tattare da illoli daban-daban da ka iya ta'azzarar masu yawaitar amfani da shi.
Babban jigon sunadari da lemun tsami ya kunsa shine sunadarin Vitamin C, wanda idan ya kai wani munzali a jikin mutum ya kan gadar da barazana ga lafiyar sa a madadin ingantuwar ta.
A sakamakon haka ne, a wani littafi Fruits of Warm Climates wallafar Julia Morton, da kuma mujallai daban-daban na kiwon lafiya suka bayyana cewa, yawan amfani da lemun tsami ya kan haifar da cututtuka da suka haɗar da:
1. Ciwon haƙori.
2. Ciwon kai na ɓari ɗaya kuma mai tsanani.
3. Tsotse ruwan jiki da kuma sanya yawan fitsari.
KARANTA KUMA: Kuɗin shiga: Hukumar kastam reshen Apapa ta samar da N31bn cikin wata guda
4. Ciwon ciki, ƙwarnafi da tashin zuciya.
5. Zafin zuciya da cutar ulcer.
6. Sanya ƙurarraji a cikin baki.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne hukumar kastam ta wani reshe a jihar Legas, ta samar da kuɗin shiga na kimanin naira biliyan 31 cikin wata ɗaya kacal.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng