Mace-macen da kansar dubura ta maza ke haifarwa, yazo ya zarta na mata na kansar mama
- Babu abinda yafi kashe maza a tsufansu irin kansar dubura, bayan ta ciki da ta huhu
- Mata kuma kan kamu da kansar nono
- An gano kansar dubura ta zarta ta nono a kisa

Masana a kasar Burtaniya, sun gano cewa, cutar kansa ta dubura na kokarin maye gurbin ta nono a tsakanin al'umma a sabuwar kididdiga.
A da dai, an fi ganin mace-mace a kansar nono fiye da ta dubura, amma saboda bincike da kiyayewa, ya sanya an iya shawo kan matsalar wadda bata da magani, sai dai neman kariya.
Kansa dai batta da magani, kuma ta fi kama manyan mutane a da, amma an zo an gane tana kama yara samari da 'yan mata.
DUBA WANNAN: Yadda Obasanjo yake yi wa Buhari taron dangi kan 2019
Ita dai kansar mama mata tafi kamawa, ita kuwa ta dubura maza tafi kamawa a masu shekaru da dattijai.
Masana na ganii idan ita ma kansar dubura an sanya mata ido da kula da karin kudaden magunguna da na bincike za'a iya shawo kanta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng