Dole masu kwana da bebin roba su bi a hankali inji kwararru
- An yi gargadi ga masu Kwanciya da ‘yar tsana
- Wasu na tarawa da bebin roba a a madadin iyali
- Yin wannan a sabawa koyarwar addini kiristanci
Mun samu labari cewa Masana sun gargadi masu tarawa da bebin roba da nufin gudun haihuwa ko wani dalili inda su kace hakan fasikanci don haka dole masu wannan aiki su tuba. Bayan haka wutar lantarki na iya jawowa mutum hadari.
Mun samu labari daga manema labari cewa wata Masaniya a harkar tazara da tsagaita haihuwa Misis Appolonia Eke ta ja kunnen masu kwanciya da ‘yar tsana mai aiki da wuta a madadin iyali da su daina don kuwa hakan ba shi da wani amfani.
KU KARANTA: An samawa Matasa miliyan 7 aiki a Gwamnatin Buhari
Masana su na ganin akwai hadari wajen kwanciya da ‘yar tsana ko duk wani abu maras rai ko kuma tarawa da mace ta kafar da ba ta dace ba. Hakan dai ya sabawa Addinin Kirista inji Appolonia don hali ne na mutanen banza kuma haramun ne.
Wannan kwararra ta kamanta kwaciya da ‘yar tsana da kwanciya da gawa wanda tace duk addini bi yarda da su ba. Kuma ma dai akwai hadari wajen amfani da lantarki a wannan yanayi. Amma tace babu laifi wajen jinkirta haihuwa saboda sha’anin lafiya.
Idan ba ku manta ba, yau ake sa rai tsohuwar jarumar nan da aka dama dasu a baya a dandalin shirya fina-finan Hausa, Abida Muhammad za ta yi aure.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng