Gwamnatin Jihar Legas za ta yi sababbin titi a cikin kananan Hukumomi
- Gwamnatin Jihar Legas za ta gina kananan hanyoyi har 181
- Gwamna Ambode ya saki kashin kudin aikin ga’yan kwangila
- A bara Ambode yayi tituna sama da 110 a cikin Unguwanni
Jiya mu ka samu labari cewa Gwamnatin Jihar Legas karkashin mai girma Gwamna Akinwumi Ambode za ta yi sababbin hanyoyi har 181 a fadin kananan Hukumomin Jihar 20.
Gwamnatin Jihar ta tabbatar da wannan a shafin ta na Tuwita inda tace har an saki kudin wannan aiki sama da Naira Biliyan 5.563. Yanzu haka ‘Yan kwangila za su fara aiki a dukkanin kananan Hukumomin Jihar inda za a gina tituna 181.
KU KARANTA: Ana sa rai a fara fitar da shinkafa zuwa Kasashen Duniya
A baya dama Kwamishinan ayyuka na Jihar Injiniya Ade Akinsaya ya bayyana cewa Gwamna Ambode zai cika alkawarin da ya dauka na gina kananan tituna a cikin gari. A bara dai an yi irin wadannan hanyoyi 114 a cikin Unguwanni.
Wannan Biliyan 5 da aka ware dai shi ne kashi 30% na kwangilar. Ana sa rai za a kashe sama da Biliyan 18.545 wajen gina wadannan hanyoyi a kowace karamar Hukuma. An raba aikin inda ake sa rai za a kammala cikin tsakiyar shekarar nan.
Dazu kun ji cewa Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari zai kashe makudan kudi wajen yin hanyoyi 9 a fadin Jihar Katsina a wannan shekarar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng