Karanta sakon da laftanar janar Buratai ya aika ma shugaban kungiyar Boko Haram
Shugaban hafsoshin rundunar Sojan kasa,Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya gargadi shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Abubakar Shekau cewa fada da aljani babu riba.
Buratai ya aika da wannan sako ne cikin wata kasida da ya rubuta a shafinsa na Facebook, inda ya shawarci Shekau ya mika kansa ko kuma ya rungumi zaman lafiya saboda a yanzu ba shi da wata hanyar tserewa.
KU KARANTA: Sakkawata sun kai kukansu gaban Sarkin Musulmi kan za’a yi musu mulkin kama karya
Legit.ng ta ruwaito Buratai yayi ma wannan kasida taken “Karya ta kare’, inda ya gargade shi cewar duk wasu akidun da yake rike da su sun kare, musamman yadda duk mukarrabansa sun tsere sun rabu da shi, sa’annan Sojoji na samun gagarumar nasara a akan yan ta’addan.
A wani labarin kuma, Sojojin Najeriya sun gano wasu tarin mantan tankokin yaki a sansanin Boko Haram bayan wani artabu da suka sha, inda suka yi ma yan ta’adda kisan kiyashi a jihar Borno.
A yayin wannan farmaki, Sojojin sun gano wata babbar motar yaki mai dauke da bindiga a cikinta, wanda mayakan Boko Haram suka taba kwacewa a baya, a zamanin da suke da karfin iko a kananan hukumomi guda 5.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng