Hijabi: Mata Musulmai sun yi kira da a kyale su su saka hijabi a ko'ina

Hijabi: Mata Musulmai sun yi kira da a kyale su su saka hijabi a ko'ina

- Kungiyar Gamayyar Mata Musulmai na Najeriya ne ta yi wannan kira a ranar Alhamis

- Wata 'yar kungiyar mai suna Hajiya Mariya Sani, ita ce ta yi kiran a taron Ranar Hijabi na Duniya a Abuja

- Ta yi kira ga wadanda lamarin ya shafa da su mutunta kundin tsarin mulki, su bar mata su sanya hijabi

Kungiyar Gamayyar Mata Musulmai na Najeriya ta yi kira da a yi gyara a tsarin sanya tufa a kowace sana'a ta yadda mata musulmai za su sanya hijabi ba tare da nuna bambamci ko tsangwama ba.

A ranar Alhamis ne wata 'yar kungiyar mai suna Hajiya Mariya Sani ta yi wannan kira yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a Abuja, a wurin taro na Ranar Hijabi na Duniya.

Hijabi: Mata Musulmai sun yi kira da a kyale su su saka hijabi a ko'ina
Mata Musulmai sun yi kira da a kyale su su saka hijabi a ko'ina

Ta bayyana cewar baya ga kasancewar sanya hijabi umurni ne daga mahalicci, sanya shi kuma kamala ce da mutumcin 'ya mace. Wanda rashin saka sa ko dokar hana saka sa kauyanci ne da rashin wayewa tunda riko ne da tsohon dabi'a da turawan mulkin mallaka su ka dasa mu a kai.

DUBA WANNAN: Gurbatattun mutane ke neman hana Buhari tsayawa takara: CACOL

Hasali ma, kundin tsarin mulki ya ba wa kowani dan Kasa damar gudanar da addinin sa da kuma riko da shi. Don haka ta na kira ga dukkan wadanda wannan lamari ya shafa da su daraja kundin tsarin mulki.

Ta ce zama dole ne ya yi su fito su yi wannan kira ganin yadda lamarin hijabi ke ta kawo cec-kuce a 'yan kwanakin nan. Ta kuma yi kira ga mata ma su sanya hijabi da su sanya shi yadda ya dace su na ma su bauta ma ubangijin su. Wadanda kuma ba su sanyawa, ta janyo hankulan su da su rinka sanyawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164