Gurbatattun mutane ke neman hana Buhari tsayawa takara: CACOL

Gurbatattun mutane ke neman hana Buhari tsayawa takara: CACOL

- Cibiyar Yaki da Rashawa da Tabbatar da Adalci (CACOL), ita ce ta bayyana hakan

- Ta ce barayin kudin al'umma ne ke neman hana Buhari tsayawa takara

- Ta kuma yi kira ga ma su kishin Kasa da su marawa Buhari baya don a fatattaki cin hanci da rashawa

Cibiyar Yaki da Rashawa da kuma Tabbatar da Adalci (CACOL), ta bayyana cewar gurbatattun mutane wadanda su ke jin radadin yaki da rashawa ne ke neman hana Buhari tsayawa takara.

Gurbatattun mutane ne ke neman hana Buhari tsayawa takara: CACOL
Gurbatattun mutane ne ke neman hana Buhari tsayawa takara: CACOL

Cibiyar ta yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis ta bakin Shugaban ta, Mista Debo Adeniran, a inda ya ce yaki da rashawa da Buhari ke yi ya hana barayin dukiyar al'umma sakat.

Adeniran ya ce sakamakon rashin sassaucin da barayin su ke fuskanta ne ya sa su ke bin duk wata hanya da za su iya bi don ganin sun hana Buhari karisa shekarun sa ballantana ma ya nemi sake fitowa.

DUBA WANNAN: Rikicin jihar Benuwe: An damke mutane 24, an gurfanar da wasu 19 kotu

Ya kuma ce lambar yabo da Kungiyar Afirika (AU), ta ba wa Buhari na kiran sa Gwarzon Yaki da Rashawa a Afirika, ya nuna cewar Buhari ba wasa ya fito yi ba.

Adeniran ya yi kira ga 'yan Najeriya ma su kishin Kasa da su marawa Buhari baya don a fatattaki cin hanci da rashawa don a cewar sa, ya ki da cin hanci da rashawa ba aikin gwamnati ne kadai ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164