Hukumar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane tare da 'yan fashi da makami 38 a jihar Kaduna
Cikin watanni uku da suka gabata, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ta cafke 'yan ta'adda 38 da suka shahara da aikata laifukan garkuwa da mutane tare da fashi da makami.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Austin Iwar, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ranar larabar da ta gabata, inda yace an cafke wannan miyagu ne a tsakanin watan Oktoba na shekarar 2017 da watan Janairun shekarar 2018.
Mista Austin yake cewa, cikin miyagu 38 da hukumar ta cafke, akwai 21 masu aikata laifukan fashi da makami da kuma garkuwa da mutane, sai kuma ragowar 17 da suka shahara da sara suka a cikin birnin jihar.
Yake cewa, akwai muggan makamai 41 tare da motoci uku da hukumar ta samo wajen wannan 'yan ta'dda, inda ya tashi kafada da cewar, babbar nasarar da suka samu shine cafke 'yan fashi da makami da suka addabi hanyar garin Zaria zuwa Kano.
KARANTA KUMA: Siyasar Kano: Cacar baki tayi tsanani tsakanin Misau da Barau akan Kwankwaso
Kwamishinan ya kara da cewa, hukumar ta cafke 'yan sara sukar ne a unguwannin hayin Rigasa, Tudun Wada, da kuma unguwar Rimi wanda dukkanin su a tantagwaryar birnin jihar suke, inda suke bai wa hukumar rahotanni masu muhimmanci da za su taimaka wajen ci gaba da gudanar da bincike.
Legit.ng ta fahimci cewa, nan ba da jima wa ba hukumar za ta gurfanar da su a gaban kuliya, inda za ta yanke musu hukunci daidai da laifukan da suka aikata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng