Kotu ta tursasa wa 'yan Shi'a biyaya ga dokokin Gwamnatin Jihar Sakkwato

Kotu ta tursasa wa 'yan Shi'a biyaya ga dokokin Gwamnatin Jihar Sakkwato

- Kotu ta yi wannan umurni ne yayin gudanar da shari'a a tsakanin kungiyar 'yan shi'a da Gwamnatin Jihar Sokoto

- Kungiyar ta maka Gwamnatin Jihar da wasu mutane 6 a kotu ta na ikirarin sun tauye ma 'yan kungiyar hakkokin su

- Kungiyar ta kuma nemi da a biya su diyyar naira miliyan 50 bisa wannan cutarwa da a ka mata

Babban Kotun Tarayya a Sokoto ta umurci 'Yan Shi'a da su bi dokokin Jihar Sokoto a kan Addinai. Ta yi wannan umurni ne a yayin gudanar da shari'a a tsakanin kungiyar da Gwamnatin Jihar da wadansu mutane 6 wadanda kungiyar ta shigar da kara a kan su.

Kotu ta tursasa wa 'yan Shi'a biyaya ga dokokin Gwamnatin Jihar Sakkwato
Kotu ta tursasa wa 'yan Shi'a biyaya ga dokokin Gwamnatin Jihar Sakkwato

Kungiyar ta shigar da karar ne ta na me zargin Gwamnatin da tauye ma 'yan kungiyar hakkokin su na kasancewa 'yan Kasa. Sakamakon haka ne ta bukaci Gwamnatin ta biya ta diyyar naira miliyan 50 bisa wannan cutarwa da ta ke ikirari.

KU KARANTA: Wani yaro da bai isa tuki ba ya halaka wata daliba da wadan su mutane biyu a Gusau

Sai ga shi a ranar Laraba, Alkali mai shari'a Saleh Idrissa ya bayyana cewar Hukumar 'Yansanda ta na da iko da hakkin kare jama'a da dukiyoyin su. Su kuma 'yan shi'a su na da damar gudanar da addinin su na shi'a matukar ba za su shiga hakkin sauran jama'a ba.

Sai dai kuma ya yi watsi da neman a biya ta diyya da ta yi. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar wadanda su ka shigar da karar a madadin kungiyar su ne, Farfesa Shehu Maigandi da Malam Kasimu Mohammed da kuma Malam Sidi Mannir.

Karar kungiyar ta fada ne a kan Gwamnan Jihar na Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da Alkalin Alkalai na Jihar, da Darakta na Jihar, da Sifeta Janar na 'Yansanda da kuma Daraktan DSS na Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164