Ziyarar jihar Kano: Ja da baya ba tsoro bane gyaran taku ne – Inji Sanata Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewar shuwagabanni a jihar Kano, da shuwagabanni a Abuja ne suka bashi shawara akan ya fasa ziyarar jihar Kano don gudun rikici.
BBC Hausa ta ruwaito Sanata Kwankwaso yana fadin akwai hadin bakin hukumar Yansandan jihar Kano, da wasu shuwagabannin a Kano da Abuja da suka hada baki don ganin sun tayar da hankali a yayin ziyarar da zai kai jihar, hakan ya sanya Kwankwaso fadin shugabancin Yansanda na bukatar garambawul.
KU KARANTA: Ziyarar Kwankwaso: Ban yi mamaki ba, dama can na san matsoraci ne – Inji Ganduje
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana fadin “idan muka samu sabuwar gwamnati mai jin shawara, lallai sai mun yi ma shugabancin rundunar Yansandan Najeriya garambawul, don yi mata seti.”
Saurari hirasa:
Da aka tambaye shi ko fitowar Yansandan ne ya bashi tsoro, sai Kwankwaso yace “Ja da baya bai zam tsoro ba, kuma idan suna takama da Yan siyasa da suka fito da rundunar su ne, muma muna da yan siyasa a irin wannan tsari, zamu shiga Kano, kuma za muyi taron da ya ninka wannan yawa.”
Daga karshe tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa rashin shigarsa jihar Kano alheri ne, don baya so ace saboda shi an ji ma wani rauni, an wulakanta wani, ko kuma a ci mutuncin wani.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng