Jam’iyyar PRP na shirin dawowa da karfin ta domin tika APC da kasa

Jam’iyyar PRP na shirin dawowa da karfin ta domin tika APC da kasa

- Wasu manyan ‘Yan siyasa na ta kokarin tada Jam’iyyar PRP

- Jam’iyyar adawar ta fara samun karbuwar Jama’a har a Kudu

- Manyan ‘Yan Jam’iyyar na shirin kada Shugaba Buhari a 2019

Mun samu labari cewa wasu tsofaffin Ministoci da manyan ‘Yan siyasan Najeriya na shirin tada Jam’iyyar adawa ta PRP domin yi wa Jam’iyyar APC taron dangi a zabe mai zuwa na 2019.

Jam’iyyar PRP na shirin dawowa da karfin ta domin tika APC da kasa
Jam'iyyar PRP ta fara samun karbuwa a Kasar Inyamurai

A jiya Daily Trust ta rahoto cewa a makon gobe ake sa ran wasu manyan ‘yan siyasa sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar adawar da Marigayi Malam Aminu Kano ya kafa ta PRP inda za a fara shirin tsaida ‘dan takarar Shugaban kasa.

KU KARANTA: APC tayi magana game da alkawuran da ta dauka

Jam’iyyar ta PRP ta fara shiryawa zaben 2019 domin ganin ta tika Shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC da kasa. Jama’a da dama dai nayi wa Jam’iyyar kallon Jam’iyyar Yankin Arewacin kasar nan tun a lokacin da aka kafa ta.

Yanzu dai manyan ‘Yan PRP na kokarin fito da Jam’iyyar a matsayin ta kasa duka domin samun karbuwa a fadin kasar. Yanzu haka mun ji cewa Jam’iyyar ta fara samun shiga har a wajen Inyamurai wanda zai ba ta damar nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng