Cutar masassarar Lassa ta halaka mutane 21, ma'aikatan lafiya 10 a Najeriya
- Cutar masassarar Lassa ta halaka mutane 21, ma'aikatan lafiya 10 a Najeriya
- Shugaban cibiyar bincike da kuma hana yaduwar cututtuka ta kasar Najeriya ta bayyana haka
- Kawo yanzu ma dai an samu bullar cutar a jihohi da dama na kasar
Shugaban cibiyar bincike da kuma hana yaduwar cututtuka ta kasar Najeriya mallakin gwamnatin tarayya watau Nigeria Centre for Disease Control (NCDC) a turance mai suna Dakta Chikwe Ihekweazu ta sanar da mutuwar mutane da dama a halin yanzu ta dalilin cutar masassar Lassa.
KU KARANTA: Gwamnati ta ba zata lamunci kisan mutane ba - Buhari
Shugabar cibiyar dai ta bayyana cewa ya zuwa yanzu akalla mutane 21 ne suka mutu yayin da kuma wasu ma'aikatan lafiyar kasa akalla 10 suka kamu da cutar a fadin kasar nan.
Legit.ng ta samu cewa kawo yanzu ma dai an samu bullar cutar a jihohi da dama na kasar sannan kuma mutane akalla 77 an gwada su suna dauke da cutar kuma yanzu haka an killace su suna karbar magani.
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Benue dake a arewa ta tsakiyar Najeriya ta sanar da rufe akalla makarantun sakandare 2,219 dake a fadin jihar saboda dalilai na rashin inganci na kwararrun malamai da kuma kayayyakin aiki.
Kwamishinan Ilimi na jihar mai suna Farfesa Dannis Ityavyar shine ya sanar da hakan ga manema labarai yau Talata a garin Makurdi, babban birnin jihar yayin da yake jawabi a gaban 'yan majalisar jihar game da yanayin ilimi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng