Gobara tayi sandiyar mutuwar dalibin makarantar Sakandare a Sakkwato

Gobara tayi sandiyar mutuwar dalibin makarantar Sakandare a Sakkwato

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau a makarantar sakandiren kwana ta Sultan Tambari dake jihar Sokoto, ta yi sanadiyar mutuwar wani dalibi mai shekaru 17 tare da jikkata wani dalibin.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewar gobarar ta fara ci ne tun misalin karfe biyu na dare tare da daukar sa'o'i tana ci kafin a shawo kanta.

Gobara tayi sandiyar mutuwar dalibin makarantar Sakandare a Sakkwato
Gobara tayi sandiyar mutuwar dalibin makarantar Sakandare a Sakkwato

Duk da ba'a tabbatar da abinda ya haddasa gobarar ba, wani jami'in ma'aikatar ilimi a jihar, ya alakanta tashin gobarar da haduwar wutar lantarki.

Kakakin ma'aikatar ilimi, Nura Bello, ya tabbatar da afkuwar al'amarin tare da bayyana cewar dalibin da ya mutu dan asalin garin Ambarura dake karamar Illela ne. Da yake karin haske a kan lamarin, Bello, ya ce wuta ta kone kayan dalibai 200 dake kwana a dakin.

DUBA WANNAN: Gwamnati na ba zata lamunci kisa da satar mutane ba - Buhari

"Dalibai 200 ne lokacin da wutar ta fara ci, amma marigayin ne kawai da wani dalibi daya wutar ta taba," inji Bello.

Ya kara da cewar, marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan ya koma dakin domin fitar da wasu kayansa.

Kwamishinan ilimin jihar, Dakta Jabbi Kilgori, ya umarci shugaban makarantar da ya binciko abinda ya haddasa gobarar.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci makarantar da gobara ta afku. Ya jajantawa iyayen dalibin da ya mutu tare da dauka alkawarin basu tallafin kudi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164