Siyasar Kano: Yadda abubuwa su ka tabarbare tsakanin Ganduje da Kwankwaso
- Ganduje ya raba gari da tsohon Maigidan sa bayan ya karbi mulki
- Gwamnan mai ci yace Gwamnatin Kwankwaso ta tafka aika-aika
- Dr. Ganduje ba su ga maciji yanzu da tsohon Gwamna Kwankwaso
Yayin da abubuwa su kayi kamari a Jihar Kano a fagen siyasa, mun kawo maku silar rikicin Gwamnan Jihar da ke kan gadon mulki Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwanaki Jaridar Daily Trust tayi wani nazari inda tace ba a wuce watanni 5 daga mikawa sabon Gwamna Abdullahi Ganduje mulki aka samu matsala da tsohon Gwamnan Jihar kuma mai gidan sa Rabiu Kwankwaso wanda ya zama Sanata.
KU KARANTA: Ministan Sufuri yace za a kawo karshen rashin aikin yi a Najeriya
Rikicin ya fara bayyana ne tun bayan lokacin da aka yi bikin taya Kwankwaso cika shekaru 59 a 2015. An ware wajen yin wannan biki a lokacin. Dama dai kafin nan Ganduje ya sallami duka Kwamishinonin Jihar da su ka yi aiki zuwa 2015.
Ganduje yayi aiki da Kwankwaso tun 1999 inda ya zama mai ba tsohon Gwamnan shawara bayan ya zama Minista a 2003. Kwankwaso ya guji zuwa Kano bayan ya bar mulki saboda gudun yi wa Gwamna Ganduje katsalandan a sha’anin mulki.
Gwamnatin Ganduje ta zargi Kwankwaso da janyowa Jihar makudan bashin da ya fi karfin ta sannan kuma an karkatar da wasu kudi na ‘Yan fansho. Ganduje ya koka da cewa shi a aka bari da biyan wannan kudi da kuma wasu da aka sace.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng