Ka fada ma al'umma adadin kudin da Wammako ya bar maka: Bafarawa ga Tambuwal

Ka fada ma al'umma adadin kudin da Wammako ya bar maka: Bafarawa ga Tambuwal

- Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya kalubalaci Gwamna Tambuwal ya bayyana wa al'umma adadin gudin da ya gada daga Gwamnatin Wammako

- Bafarawan ya yi zargin cewa Tambuwal na ganin girman Wammako ne shi yasa bai fito filli ya bayyanawa al'umma ba

- Bafarawan ya shawarci Gwamna Tambuwal da ya cire kunya ko girma ya fede ma jama'a biri har wutsiya domin mulkin ana yin ta don jama'a ne

Jigo a jami'iyyar PDP kuma Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya kalubalance Gwamna Aminu Waziru Tambuwal ya fito filli ya bayyanawa al'umma adadin kudaden da ya gada lokacin da ya karbi mulki a 2015.

Bafarawan ya yi ikirarin cewa Wamakko ya yi wa Tambuwal dabaibayi har ta zamar masa tarnaki, don hakan ne ya ke neman Tambuwal ya fito ya bayyana abin da Gwamnatin Wamakko ta bar masa.

Ka fada ma al'umma adadin kudin da Wammako ya bar maka: Bafarawa ga Tambuwal
Ka fada ma al'umma adadin kudin da Wammako ya bar maka: Bafarawa ga Tambuwal

Har ila yau, Bafarawan ya bayyana cewa canjin da talakawan Najeriya suka samu na kara dilmiya cikin mawuyacin halin rayuwa ne tare da cewar Shugaba Muhammadu Buhari ma ya san abin da kasar ke ciki.

DUNA WANNAN: Sojojin Saman Najeriya sunyi sanadiyar mutuwar 'yan Najeriya da dama - Amnesty International

Bafarawa ya ce lokacin da zai mika mulki da Wammako, ya bar masa tsabar kudi naira biliyan 12 a asusun jihar duk da cewa ya yi aiki sosai a wannan lokacin, hakan ya sa ya ke neman Tambuwal din ya fito ya bayyana ma duniya abin da aka bar masa.

Bafarawan ya yi ikirarin cewa shiru da akaji Tambuwal ya yi alama ce da ke nuna cewa akwai babbar matsala a kasa amma saboda yana kunya da ganin girman Wammako shi yasa ya yi tsit. Ya tunatar da Tambuwal cewa mulki fa anayi don jama'a saboda hakan ya kamata a cire kunya a bayyana ma jama'a gaskiya.

A yayin da yayi tsokaci kan rikicin Manoma da Makiyaya, Bafarawa ya ce siyasa ce ta shiga cikin lamarin shi ya sa ta kazanta hakan, ya kara da cewa makiyaya sanda aka san su dashi ba bindiga ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164