Zalunci ne hana ni zuwa Jihar Kano – Inji Sanata Rabi’u Kwankwaso

Zalunci ne hana ni zuwa Jihar Kano – Inji Sanata Rabi’u Kwankwaso

- Sanata Rabiu Kwankwaso yayi hira da Gidan yada labarai na BBC a daren jiya

- Kwankwaso yace azzalumai ne masu rike da mukamai su ka hana shi zuwa gida

- Sanatan na Kasar yace ya ji shawarar manya ne ya janye tafiyar sa saboda tsaro

Jiya mu ke jin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano ya bayyanawa Rabiu Musa Kwankwaso BBC cewa Azzalumai ne su ka hana shi zuwa Jihar sa ta Kano duk da yana matsayin Sanata mai wakiltar Jihar.

Zalunci ne hana ni zuwa Jihar Kano – Inji Sanata Rabi’u Kwankwaso
Ina Sanata an hana ni shiga Kano wulakanci ne - Kwankwaso

A cewar Sanatan a wani bidiyo da ya bayyana jiya daga gidan BBC, wasu Makiya ne su kayi kutun-kutun wajen ganin an hana shi lekawa ya ga mutanen sa da iyayen sa da sauran mutanen arziki wanda yace hakan na da hadari babba a siyasa.

KU KARANTA: Siyasar Kano: An yabawa Kwankwaso na janye taron sa

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya nuna cewa ja da da baya ba tsoro bane kuma komai da lokacin sa. Kwankwaso yake cewa, manyan Shugabanni da sauran Jama'a ne su ka kira shi su ka nemi a zauna da lafiya don haka ya dage zuwan sa.

A cewar babban ‘Dan siyasar lokacin zuwan sa na nan zuwa kuma komai ba-jima-ko-bade zai shiga Garin Kano. A cewar sa har gobe babu wanda zai canza ra’ayin sa game da shi, sai dai ma wasu su kara shiga Kwankwasiyya saboda wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: