Ina alfahari da zama Direban Sheikh Zakzaky - Farfesa Danladi

Ina alfahari da zama Direban Sheikh Zakzaky - Farfesa Danladi

- Farfesa Danladi yace yana alfahari da zama Direban Shugaban Shia

- Shehin Malamin Jami'ar yace babu aibu wajen bautawa jagoran sa

- Danladi yace aikace-aikacen sa ba su hana shi koyarwa a Makaranta

Farfesa Abdullahi Danladi wani babban Malami a Jamia'ar Ahmadu Bello ta Zariya ya bayyana yadda yake alfahari da zama Direban Sheikh Yakubu El-Zakzaky na Kungiyar IMN ta Shia'a.

Ina alfahari da zama Direban Sheikh Zakzaky - Farfesa Danladi
Direban Jagoran Shia Sheikh Zakzaky Farfesa ne a ABU

A wata hira da ta bayyana kwanakin baya a Jaridar New Telegraph, Farfesa Danladi yace ba ya jin komai don yana yi wa Babban Malamin addini irin Sheikh Zakzaky wannan bauta da yake yi. Danladi yace Malamin gwarzon sa ne.

KU KARANTA: Buhari zai iya barin mulki bayan 2019 - El-Rufai

Babban Farfesan yace hakan ba ya ba shi wahala ganin cewa ga shi Shehin Malami a babbar Jami'a. Danladi yake cewa kwanan nan ya sauka daga Shugaban sashen sa na fasahar tufafi kuma ya san yadda yake tsara lokutan sa.

Danladi Abdullahi yana daga cikin Mabiya addinin na Shia amma Ubangiji ya tsaga da rabon sa ba a kashe iyalin sa ba lokacin da takkadamar 'Yan Kungiyar ta tashi da Rundunar Sojojin Najeriya, a lokacin yace shi ma yayi tafiya zuwa Iran.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng