Takkadamar Kwankwaso da Ganduje: Wasu yan siyasan Kano uku na shirin kaiwa Kwankwaso hari – Kwankwasiyya
Kungiyar Kwankwasiyya tana tuhumar cewa wasu manyan yan siyasan Kano uku na shirin kaiwa babban shugabanta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, hari idan ya zo jihar.
A wani hira da yan jarida ranan Asabar, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr Rabi'u Sulaiman Bichi, yace cikin yan siyasa akwai kwamshanoni 2; Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, Alhaji Abdullahi Abbas da kuma Alhaji Abdulmajid Danbalki Commander.
Kana Dakta Bichi ta tuhumci kwamishanan jihar Kano, Alhaji Rabi'u Yusuf, da nuna son kai ta hanyar nuna goyon bayansa karara ga gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Yace: “Abune sannane a jihar Kano tun watan Nuwanban da ya gabata cewa Sanata Kwankwaso ya shigo jihar Kano. Amma gwamnatin jihar ta Iliyasu Kwankwaso, Abbas, da Kwamanda sun lashi takobin hanashi zuwa.”
KU KARANTA: Shugaba Buhari ne kadai ba barawo ba a Najeriya – Lauretta Onochie
Ya bayyana cewa a ranan 16 ga watan Disamba 2017 da 15 ga watan Junairu 2018, Iliyasu Kwankwaso ya fada a gidajen rediyon Express da Pyramid cewa ba zasu taba bari Sanata zuwa jharba kuma yace idan har Kwankwaso ya zo, sai sun shirya taro domin shi.
Kana shi kuma Kwamanda ya yi a a tashan Aminci FM da FRCN Kaduna cewa idan Kwankwaso ya sake ya shigo jihar Kano sai an daure shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng