Duba hotunan El-Rufa'i a kasar Saudiyya domin addu'o'i ga Najeriya
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’I, yanzu yana kasa mai tsarki tare da wasu jami’an gwamnatinsa. Gwamnan, kamnar yadda ya saki hotunansa a shafinsa na Tuwita, ya ce yana kasar ta Saudiyya ne domin gudanar da addu’o’i na musamman ga Najeriya da shugaba Buhari.
Daga cikin masu rakiyar gwamnan, akwai mai taimaka masa na musamman, Uba Sani, mutumin da rahotanni ke kishin-kishin din cewar gwaman na son maye gurbin sanatan Kaduna ta tsakiya, Kwamrad shehu Sani, da shi.
DUBA WANNAN: Kwamitin El-Rufa'i ya gabatar da rahotonsa ga uwar jam'iyyar APC ta kasa
Saidai Sanata Shehu Sani ya bayyana yunkurin hakan da cewar rashin lissafin siyasa ne tare da bayyana cewar shine keda goyon bayan jama'ar jihar Kaduna ta tsakiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng